1 Nuwamba 2020 - 14:29
Wani Bom Mai Karar Gaske Ya Fashe A Birnin Bagadaza

Tashar talabijin din “al-mayadeen”ta bayar da rahoton dake cewa; An ji kasar fashewar wani abu mai kara a cikin babban birnin kasar ta Iraki a daren jiya Asabar.

ABNA24 : Wata majiyar labarai ta ál-Sahfaq’a kasar ta Iraki ta ambaci cewa majiayar tsaro ta shaida mata cewa; Bom din ya tashi ne a kusa da wani wurin sayar da barasa a yankin Karrada dake cikin Bagadaza.

Kawo ya zuwa yanzu dai an tabbatar da jikkatar mutum daya sanadiyyar tashin bom din.

Babu watakungiya wacce ta dauki alhakin kai harin.

Iraki dai ta yi fama da kungiyoyin ‘yantaádda a baya, da su ka kunshi al-kaída da Daesh, kafin kungiyoyin sa-kai na “Hashdusshaábi su murkushe su.

342/